A daidai lokacin da ake ci gaba tattauna batun yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, mutanen zirin sun fara mayar da hankalinsu ne kan sake gina yankin da ganin yadda za ta kaya a yunƙurin.
Manyan motoci suna ta share hanyoyi suna kwashe baraguzai domin tsabtace titunan yankin wanda a baya yake cike da mutane amma yanzu suka zama kufai.Wasu sassan zirin yanzu baki ɗaya ya ruguje, ta yadda suke da wahalar ganewa.
"Nan ne wajen da gidana yake," in ji Abu Iyad Hamdouna a lokacin da yake nuna wani tulin baraguzai a yankin Sheikh Radwan da a baya ya ke cikin wuraren da suka fi mutane a zirin.
"A nan gidan yake, amma yanzu babu ko alamar gida."
Abu Iyad datijo ne mai shekara 63. Ya ce idan ma Gaza za ta sake komawa hayyacinta, yana tunanin da wahala ya yi tsawon rayuwa da zai shaida hakan.
"Ina tunanin za a yi aƙalla shekara 10 kafin a sake gina zirin nan. Wataƙila lokacin mun mutu. Za mu rasu ba tare an kammala sake ginin ba."
Shi ma Nihad al-Madhoun mai shekara 43 da ɗanuwansa Said suna ta ƙoƙarin share rusasshen gidansu ne.
"Share baraguzan ƙadai zai iya cin shekara biyar,"
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta an yi asarar kusan fam biliyan 53 wato kimanin dala biliyan 70 a zirin. Kusan gidaje 300,000 ne aka lalata, kamar yadda hotunan tauraron ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya wato Unosat ya nuna.
Yanzu haka akwai aƙalla tan miliyan 60 na baraguzai a Zirin Gaza, kuma akwai bama-bamai da gawarwaki a cakuɗe da baraguzan.
An kashe aƙalla mutum 68,000 a Gaza a cikin shekara biyu da suka gabata, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas ta bayyana, amma Majalisar Ɗinkin Duniya na amincewa da ƙididdigarta.
Zuwa yanzu dai ana cike da tunani da ruɗu ne kan ta ina za a fara aikin.
Amma mutanen Gaza da muka zanta da su suna ɗar-ɗar da tsare-tsaren da aka shirya daga ƙasashen waje, kuma suna da nasu tsare-tsaren.
Yanzu tambayar ita ce wane ne zai jagoranci aikin sake gina zirin?
Tsare-tsaren da aka yi
Yahya al-Sarraj, magajin garin Gaza da Hamas ta naɗa yakan fito yana rangadin zirin. Yanzu haka shagunan sayar da abinci da sauran buƙatu sun fara buɗewa.
Sai dai Gaza ta saba da irin wannan yanayin, in ji shi, inda ya tuna irin rikice-rikicen da aka yi a baya.
"Mun samu labarin akwai tsare-tsaren da ake yi a ƙasashen waje da na cikin gida da na yanki. Amma muna da namu tsarin."
"Muna kiran tsarinmu da 'Phoenix of Gaza."
Wannan ne tsarin cikin gida da Falasɗinawa suka shirya domin sake gina garinsu.
"Muna so mu cike gurbin ne," in ji Yara Salem, tsohon manaja a bankin duniya.
"Ba zai yiwu ba ka jira tsare-tsaren da aka ƙaƙaba maka ba tare da kana da naka tsarin ba."
Tsarin na Phoenix plan wanda aka fitar a watan Fabrailou, wani tsari ne da ƙwararrun Falasɗinawa kusan 700 suka zauna suka tsara.
Sai dai ba a sa Hamas ba a cikin waɗanda aka tattauna da su domin tsare sabon shirin na sake gina zirin.
Sai dai tsare-tsarensu sun sha bamban da tsarin "Gaza Riviera", wanda Shugaban Amurka Donald Trump ya fara ambatawa a watan Fabrailu a ganawarsa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Amfani da AI wajen tsara zirin
Wasu takardu da aka fitar ta bayan fage a watan Agusta sun nuna yadda aka yi amfani da fasahar zamani wajen tsara irin yadda Trump yake so Zirin Gaza ya koma nan da shekara 10.
An tsare zirin ya ƙunshi yankuna da tsararrun birane cike da ababen more rayuwa a ciki.
A cikin tsarin akwai "canja waje" da aka tsara idan ɗan Gaza yana so, inda ake tunanin kusan rubu'in ƴan Gaza za su bar zirin, amma duk wanda ya amince zai tafi, za a ba shi fam 5,000 kimanin dala 3,780 da kuma samun haya mai sauƙi a ƙasashen waje.
Wannan na cikin abubuwan da ya sha bamban da tsarin Phoenix, wanda aka tsara kare muradun ƴan Gaza.
Asalin Gaza'
Bayan waɗannan fitattun tsare-tsaren guda biyu, akwai wasu. Daga ciki akwai wanda Masar ta yi magana a kai a taron sake gina Gaza da ƙasashen Larabawa suka yi a Cairo a watan Maris.
Wannan tsarin ya ɗan kama da na Falasɗinawa wajen buƙatar a sanya ƴan Gaza cikin kowane tsari da za a yi.
Ita ma gwamnatin Falasɗinu a ƙarƙashin Mahmoud Abbas na tsare nata, ciki har da yunƙurin faɗaɗa Gaza da sake haɗa ta Gaɓar Yamma a ƙasar Falasɗinu a nan gaba.
Tafiya sannu, kwana nesa
Da alamu dai aikin zai ci lokaci, kamar yadda Shelly Culbertson ta bayyana aikin da "sake gina birnin cikin sannu."
"Aikin sake gina zirin a lokacin da mutane suka zai taimaka wajen tabbatar da tsari mai kyau," in ji ta
"Amma wasu wuraren sun yi matuƙar lalacewa da sai dai a ƙarasa ruguza su, sannan a sake gini daga farko.
Don haka ba maganar shekara biyar ya kamata a yi ba, wataƙaila a ɗauki gomman shekaru ana yi."
Hukumomi a Falasɗinu na ganin za a iya gaggawar aikin, amma sai da tabbacin tsaro da tabbacin cika alƙawari, musamman buɗe bakin iyakoki domin shiga zirin da kayayyakin gini.
Masar na so ta shirya taron sake gina Gaza, amma har yanzu ba a saka rana ba, kuma ƙasashen da ake tunanin za su ɗauki nauyi su ne Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, waɗanda dole za su buƙaci tabbacin cewa kuɗaɗen da za su kashe ba za su faɗa cikin wani sabon yaƙi ba.
Amma duba da yadda gwamnatin Isra'ila take ƙara nanata rashin amincewa da kafa ƙasar Falasɗinu, abin Saudiyya ke nema, ke nan akwai sauran rina a kaba.
Isra'ila ta bayyana a baya cewa ba ta da matsala idan wasu ƙasashe suka taimaka wajen sake gina Gaza, har da ma yankunan da ke ƙarƙashin sojojin Isra'ila.
Amma a kwanakin baya, Jred Kushner ya ce za a fara aiki ne a yankunan da sojojin Isra'ila ke kula da su, ba za a yi aiki ba a yankunan da ke ƙarƙashin ikon Hamas.
Amma a yankin Sheikh Radwan, Abu Iyad Hamdouna matsalarsa daban.
"Ana ta maganar sake gina gari, yaya batun ruwan sha?"
Bayan tursasa shi barin gida sau biyar saboda yaƙi, Abu Iyad burinsa kawai ya samu inda zai zauna ko ma ina ne.