Shirin Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa ana samun karuwar yunwa a duniya sakamakon raguwar samar da tallafin jinkai ga kasashen masu fama da talauci.
Shirin na WFP ya ce kimanin mutum miliyan dari uku da sha takwas ne za su yi fama da yunwa a shekarar 2026 mai kamawa.
Ya ce tsanani rashin abinci da ake fama da shi a Gaza da Sudan ya zama wajibi a kaucewa ci gaba da hakan a karni na ashirin da daya.
Amurka da sauran kasashen da ke samar da agaji a duniya sun rage yawan kudaden tallafi da suke samarwa Shirin Samar da Abincin na Majalisar Dinkin Duniya da kuma ake ganin babban gibi ne a bangaren yaki da yunwa da talauci a duniya