Tuni dai ƴan najeriya suka fara musayar yawu bisa rahotanni da ke yawo dangane da zargin sauya ko kuma yin cushe a dokar haraji ta Najeriya da ake sa ran za ta fara aiki a ranar 1 Janairu 2026.
Ɗan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Sokoto Abdulsammad Dasuki ne dai ya ja hankalin majalisar kan abin da ya bayyana da bambance-bambance da ya ce ya gano a tsakanin ƙudurin dokar haraji da majalisar ta amince da shi, da kuma wanda aka sanya wa hannu ya zama dokar da za a yi amfani da ita.A watan Yunin 2025 ɗin ne dai Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin dokokin haraji huɗu a wani mataki na sauya fasalin tsarin karɓa da tattara haraji na ƙasar.
Gwamnatin ta ce sabbin dokokin za su sauƙaƙa tsarin, da rage wahalhalun haraji kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni, da kuma taimakawa wajen inganta karɓar haraji.