Al'ummar garin Nahuce da ke jihar Zamfara na cikin alhini bayan wasu gungun ƴan bindiga sun sace mata sama da 20 da ƙananan yara da suke goyo da kuma wasu maza huɗu.
Wani abu da ya fi tayar wa al'ummar hankali shi ne yadda ɗaya daga cikin matan da aka sace ta haihu a hanyar tafiya da su daji, amma duk da haka maimakon ɓarayin su bari ta koma, ai suka tafi da ita.Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka muhawara kan samun sauƙin matsalolin tsaro musamman a arewacin Najeriya, inda wasu ke ganin an samu sauƙi, wasu kuma suke ganin har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cikin jihohin da suke daɗe suna fama da matsalar garkuwa da mutane da fashin daji da kashe-kashe, lamarin da ya yi ajalin mutane da dama.