Zanga-Zanga A Bangladesh: Rikici Ya Kaure Bayan Rasuwar Dan Gwaggwarmaya Sharif Hadi

 Hankula sun tashi a ƙasar Bangladesh bayan ɓarkewar rikici a yayin zanga-zanga da aka gudanar, sakamakon rasuwar wani fitaccen ɗan gwagwarmaya mai suna Sharif Hadi. Mutuwar tasa ta ƙara rura wutar fushin jama’a, inda aka samu tarzoma a sassa daban-daban na ƙasar.

Zanga-Zanga A Bangladesh

Shaidu sun ce zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali ne bayan labarin rasuwar Sharif Hadi ya bazu, lamarin da ya sa masu zanga-zangar suka yi arangama da jami’an tsaro. An rawaito cewa an kona motoci, an lalata kadarori, kuma an ji rauni a tsakanin jama’a da jami’an tsaro.

Gwamnati ta ayyana cewa tana binciken musabbabin mutuwar Sharif Hadi, yayin da ta zargi wasu ƙungiyoyi da amfani da lamarin wajen tayar da fitina. A ɓangaren nasu, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na zargin jami’an tsaro da amfani da ƙarfin tsiya fiye da kima wajen tarwatsa masu zanga-zanga.

A halin yanzu, an ƙara tsaurara matakan tsaro a manyan biranen ƙasar, tare da kiran jama’a da su kwantar da hankalinsu yayin da bincike ke gudana. Rikicin dai na ƙara jaddada matsin lambar siyasa da ke addabar Bangladesh a wannan lokaci.

Post a Comment

Previous Post Next Post