Ƴan Najeriya sun daɗe suna tambayar ina ƴanbindiga da sauran masu tayar da ƙayar baya a ƙasar suke samun makamansu, lamarin da ya sa wasu suke zargin akwai lauje cikin naɗi.
An sha ganin manyan makamai a hannun ƴanbindigar, musamman a baya-bayan nan inda suke nuna makamansu a kafofin sada zumunta domin bayyana wa duniya irin ƙarfin da suke da shi.Baya ga samun irin wadannan makamai ta hanyar masu safarar su ta barauniyar hanya, lokaci zuwa lokaci wadannan ‘yan bindiga kan kai hari kan jami’an tsaro, kuma idan suka yi nasara sukan kwashe makamansu, waɗanda ake zargin suke amfani da su wajen ci gaba da kai hare-hare.
To amma wadanne bindigogi ne wadannan ‘yan bindiga ke amfani da su wajen kaddamar da hare-hare kan al’umma, musamman a arewacin Najeriya?