Ministan Abuja babban birnin Najeriya ya ce bai yi nadamar goya wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu baya ba tun daga 2022, duk da kasancewarsa ɗan jam'iyyar PDP mai adawa.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Nyessom Wike ya ce ya ɗauki matakin ne "bisa dacewa da ɗabi'a da kuma aƙidarsa", yana mai cewa "ban taɓa ɓoye goyon bayana ga Shugaba Tinubu ba tun daga farko".Ministan ya bayyana haka ne yayin taron bikin cikarsa shekara 58 da haihuwa yau Asabar a Abuja, wanda ya samu halartar 'yansiyasa daga jam'iyyu daban-daban.
Wike ya goyi bayan Tinubu ne bayan samun saɓani da shugabannin PDP ana dab da zaɓen 2023, rikicin da ya kai shi ga zama minista a gwamnatin APC wanda kuma har yanzu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.