Sojoji 11 da suka maƙale tare da jirgi ƙirar C-130 a ƙasar Burkina Faso na kan hanyarsu ta zuwa Portugal inda tun farko can suka dosa.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ya ce Burkina Faso ta ƙyale su su bar ƙasar, inda da ya ce za su fara isa birnin Accra kafin daga bisani su ƙarasa zuwa ƙasar da suka nemi zuwa wato Portugal.Wata tawaga daga Najeriya ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin waje Yusuf Tuggar ce dai ta je birnin Ouagadougou inda ta tattauna da shugaban ƙasar Kyaftin Ibrahim Traore.a kan sojoji, bayan sama da mako ɗaya da faruwar lamarin,
A daren ranar Litinin ɗin 8 ga watan Disamba ne ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel ta AES, wadda ta ƙunshi Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar suka fitar da sanarwar yin tir da abin da suka kira keta musu sararin samaniya da wani jirgin sojin Najeriya ya yi ba bisa ƙ'aida ba.
Sai dai jim kaɗan bayan haka, hukumomin Najeriya sun fitar da nasu bayanin inda suka ce "tangarɗar na'ura ce ta sanya jirgin ya sauka a ƙasar ta Burkina Faso".
Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da Najeriya ta sanar da cewa ta kai ɗaukin gaggawa zuwa Jamhuriyar Benin, inda jiragen samanta suka daƙile ayyukan masu yunƙurin juyin mulki.