Gwamnatin Habasha tare da hukumar kula da ƴan gudun hijira da masu komawa gida da kuma shirin abinci na duniya (WFP) sun yi gargaɗin cewa shirin tallafa wa ‘yan gudun hijira a ƙasar na dab da rushewa sakamakon ƙarancin kuɗaɗe.
Sun ce idan ba a samu tallafin gaggawa ba, ayyukan ceto rayuka kamar abinci da ruwa da kula da lafiya za su tsaya cik a cikin ‘yan makonni, lamarin da zai shafi sama da ‘yan gudun hijira miliyan 1.1.Habasha, wadda ita ce ƙasa ta biyu a Afirka da ke karɓar ‘yan gudun hijira mafi yawa, na ci gaba da fuskantar ƙarin masu shigowa daga rikice-rikice a Sudan da Sudan ta Kudu, da kuma fari a Somaliya.
Duk da haka, matsanancin ƙarancin kuɗi ya tilasta hukumomin agaji rage kayan tallafin gaggawa da kashi 70 cikin 100 a shekarar 2025.
A watan Oktoba, WFP ya rage rabon abinci ga ‘yan gudun hijira 780,000 zuwa kashi 40 cikin 100 kawai.
Hukumomin sun ce rage tallafin ya haifar da ƙaruwar rashin abinci mai gina jiki a sansanonin ‘yan gudun hijira, wanda ya haura kashi 15 cikin 100.
Rahotanni sun nuna cewa mace-macen jarirai da yara ƙasa da shekara ɗaya sun kai kashi 4.7 a 2025, yayin da adadin yaran da ke fama da rashin abinci mai tsanani ya ninka fiye da sau biyu idan aka kwatanta da bara.