Ɗan wasan danben Birtaniya, Anthony Joshua ya doke Jake Paul a zagaye na shida na karawar da suka yi a birnin Miami na Amurka.
Joshua ya sha fama da Paul a karawar, saboda tsohon ɗan YouTube ɗin ya ƙi tsayawa a kara, inda ya riƙa tsalle-tsalle yana ja da gefe, amma daga baya Joshua ya gano makasar shi har ya kifar da shi sau biyu a zagaye na biyar.Paul ya sake faɗuwa a farkon zagaye na shida, kafin daga baya Joshua ya yi mashi nushi mai ƙarfin gaske da hannun dama, lamarin da ya kawo ƙarshen fafatawar da aka yi a cibiyar Kaseya ta birnin Miami.
A karshen karawar Joshua ya ce "Ina ganin wannan ba abin da na yi zato bane, ban yi bajinta ba," in ji ɗan damben mai shekara 36.
Ya ƙara da cewa "A ƙarshe dai abin da ake muradi shi ne sanya Jake Paul a tsaka mai wuya kafin kifar da shi. An ɗauki lokaci kafin hakan ta samu, amma daga ƙarshe dai an kai wajen da ake son kaiwa."
Dama dai an yi hasashen sakamakon damben zai zamo haka, amma an yi mamakin yadda aka ɗauki tsawon lokaci ana fafatawa kafin Joshua ya doke Paul ba.
Joshua ya yi nasarar lashe wasa na 29 kenan daga cikin 33 da ya fafata a rayuwarsa ta dambe, kuma a yanzu zai mayar da hankali ne ga babban ƙalubalen da ke gabansa, na karawa da Tyson Fury a shekara mai zuwa.