Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci gwamnonin ƙasar su yi biyayya ga umarnin kotun ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi ƴancin tafiyar da kuɗaɗensu.
Shugaban ya yi gargaɗi gwamnonin da ba su biyayya ga umarnin su sani cewa za su tilasta mashi zartar da wata doka da za ta ba shi ikon aikewa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu kai tsaye daga asusun kwamitin rabon arzikin tarayya.Tinubu ya yi gargaɗin ne a wajen taron majalisar zartarwar jam'iyyar APC karo na 15 a Abuja.
“Kotun ƙoli ta bayar da umarni gare ku, inda ta ce ku bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye. Idan kuka jihar har sai na yi amfani da dokar shugaban ƙasa, domin wuƙa da doya duk suna hannuna, to zan yanke ta.
“Ina matuƙar mutumta ku ne kawai, a matsayin gwamnonina. Amma idan ba ku fara aiwatar da wannan umarni daki-daki ba. za ku ga abin da zai faru,'' in ji Tinubu. .
A ranar 11 ga watan Yulin 2024 kotun ƙoli ta bayar da hukuncin da ya tabbatar da wanda buƙatar gwamnatin tarayya ta bai wa ƙananan hukumomin Najeriya ƴancin tafiyar da kuɗaɗensu.
Dukkan alƙalan kotun bakwai sun amince da hukuncin cewa riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnatocin jihohi ke yi ya saɓawa tanadin kundin mulkin ƙasa.