Dubban mutane na zanga-zanga kan kisan Shugaban Dalibai a Bangladesh

Dubban Mutane Sun Halarci Nana'izar wani fitaccen shugaban ɗalubai da aka kashe, a birnin Dhaka na Bangladesh.

An Sharif Osman Hadi ne a kai lokacin da ya ke dawowa daga sallar Juma'a, kuma ya rasu bayan jinyar kwana shida a wani asibiti a Singapore.

Mummunar zanga-zanga ta ɓarke a birnin Dhaka, inda aka shafe kwana biyu ana yin ta.

An jibge sojoji da ƴansanda domin daƙile yunƙurin tayar da tarzoma.

Gwamnati ta sanar da zaman makoki na kwana ɗaya amma magoya bayan Hadi sun ci gaba da zanga-zanga a dandalin Dhaka.

Shugaban hukumar kare ƴancin ɗan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya yi kiran a gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano masu hannu a kisan Hadi

Post a Comment

Previous Post Next Post