Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da kashe Naira biliyan 5 domin sake gina Makarantar Koyon Aikin Jinya da ke Zurmi a Ƙaramar Hukumar Zurmi, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa tsarin ba da hidimomin kiwon lafiya a faɗin jihar.
Gwamna Dauda Lawal ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin bayar da tallafin kuɗi ga mutane 850 a Zurmi. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamna, Shehu Adamu Gusau, ya fitar a ranar Asabar.Gwamnan, wanda mataimakinsa Mani Malam Mummuni Masamar Mudi ya wakilta a wajen taron, ya ce wannan mataki na nuna jajircewar gwamnatinsa wajen aiwatar da ayyukan ci gaba masu tasiri a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Gwamna Lawal ya kuma bayyana cewa an kammala shirye-shiryen rushewa tare da sake gina Fadar Masarautar Zurmi, domin kiyaye tare da bunƙasa al’adu da gadon gargajiya na al’ummar yankin.
Haka kuma, gwamnan ya bayyana cewa an bayar da kwangilar Naira biliyan 2 domin gina Titin Kanwa, yayin da ake ci gaba da aikin gina kilomita bakwai na Titin Zurmi–Rukudawa, kilomita uku na tituna a cikin garin Zurmi, da kuma kilomita uku na tituna a garin Moriki. Ya ƙara da cewa ana gyaran Cibiyar Kula da Lafiya ta Firamare ta Zurmi da Babban Asibitin Zurmi.
Gwamna Lawal ya yaba wa Kwamishinan Filaye da Gidaje, Alhaji Nasiru Ibrahim Zurmi, bisa daukar nauyin shirin tallafin kuɗin, tare da kira ga sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da su kwaikwayi wannan ɗabi’a wajen tallafa wa jin daɗin al’umma.
Tun da farko, Alhaji Nasiru Ibrahim Zurmi ya bayyana cewa shirin an tsara shi ne domin taimaka wa ƙoƙarin gwamnati na samar da tallafin jin kai da rage raɗaɗin matsin tattalin arziƙi da ke addabar mazauna yankin. Ya ce an zaɓi mutane 850 da za su ci gajiyar shirin daga rumfunan zaɓe a dukkan mazabu na Ƙaramar Hukumar Zurmi, inda kowannensu zai karɓi Naira 20,000.
A saƙonnin fatan alheri da suka gabatar, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu, da Shugaban Ƙaramar Hukumar Zurmi, sun bayyana shirin a matsayin abin yaba da kuma abin koyi ga sauran jama’a.