Majalisar dokokin ƙasar Algeria ta fara duba wani ƙudirin doka da ke neman la’anta da kuma ɗaukar mulkin mallakar Faransa a matsayin laifi. Ƙudirin ya tayar da muhawara mai zafi a cikin gida da kuma a dangantakar Algeria da Faransa.
Ƙudirin dokar na neman ayyana ayyukan da Faransa ta aikata a lokacin mulkin mallaka, wanda ya ɗauki tsawon shekaru sama da 130 a matsayin laifukan cin zarafin bil’adama, ciki har da kisa, azabtarwa, kwace filaye da kuma murkushe ‘yan gwagwarmayar ‘yanci.
Masu goyon bayan kudirin sun ce matakin yana da muhimmanci domin adana tarihi, kare mutuncin waɗanda suka mutu, da kuma tabbatar da cewa irin waɗannan laifuka ba su sake faruwa ba. Sun kuma jaddada cewa dokar za ta taimaka wajen ilmantar da matasa game da irin wahalhalun da kakanninsu suka sha.
Sai dai a ɓangaren guda, wasu na ganin kudirin na iya ƙara dagula alaƙar diflomasiyya tsakanin Algeria da Faransa, wadda tuni take fuskantar matsaloli kan batutuwan tarihi, diyya da neman afuwa kan laifukan mulkin mallaka.
A halin yanzu, ana sa ran kudirin zai ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a majalisa, yayin da idanu ke kallon martanin gwamnatin Faransa da kuma yadda wannan mataki zai shafi dangantakar ƙasashen biyu nan gaba.