Kimanin mako daya kenan da Burkina Faso ta tsare dakarun sojan Najeriya 11 bayan jirginsu ƙirar C-130 ya yi saukar gaggawa a ƙasar sakamakon matsalar da ya samu.
A ranar Litinin ta makon jiya ne ƙungiyar Association of Sahel States (AES) - wadda ta ƙunshi Burkina da Nijar da Mali - ta yi tir da abin da ta kira keta musu sararin samaniya da jirgin sojin Najeriya ya yi ba bisa ƙ'aida ba.
Har yanzu hukumomin AES na ci gaba da tsare dakarun sojan, waɗanda suka ƙunshi soja tara da ma'aikatan jirgi biyu, yayin da suka ce suna ci gaba da bincike kafin ɗaukar mataki na gaba."Muna ƙoƙarin kammala bincike game da abin da ya faru kafin mu ɗauki mataki na gaba," kamar yadda Daoud Aly Mohammedine, ministan tsaro na ƙasar Mali, ya shaida wa BBC ranar Juma'a.