Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa akwai aƙalla ƴan gudun hijira 21,807 daga ƙasashen makwabta da suka tsere wa rikici da ba a yi wa rijista ba a Najeriya, lamarin da ke hana su samun tallafin abinci da kiwon lafiya da sauran muhimman abubuwan jin-kai.
Rahoton hukumar kula da ƴan gudun hijira ta MDD UNHCR na Nuwambar 2025, ya nuna cewa mafi yawan waɗanda ba a yi wa rijista ba sun fito ne daga yankin Anglophone na Kamaru mai fama da rikici.Masu neman mafaka da ƴan gudun hijira 127,000 suka je Najeriya daga ƙasashe 41, inda 21,807 ke jiran hukumar ƙasa ta ƴan gudun hijira NCFRMI ta yi musu rijista.
A halin yanzu, akwai mutum 80,915 da aka amince da su a matsayin ƴan gudun hijira, yayin da aka tantance bayanan masu neman mafaka fiye da 25,000.
Binciken na UNHCR ya nuna cewa adadin ƴan gudun hijira da ba a yi wa rijista ba ya ƙaru cikin shekara guda, daga 21,095 a Disambar 2024 zuwa 32,750 a Yuni 2025, kafin ya sake sauka zuwa 21,807 a Nuwambar 2025.
Ƴan gudun hijira da ba a yi wa rijista ba dai ba su da damar samun tallafin abinci ko kuɗi ko inshorar lafiya da sauran tallafin jin-kai daga UNHCR.