Wasu sanannun ’yan majalisar dattawa na Amurka (US Senators) sun gabatar da wani ƙudiri na doka da nufin hana shugaban ƙasar, Donald Trump, ko duk wani shugaban Amurka nan gaba, daga yin yunƙurin ƙwace ko siyan Greenland ko amfani da ƙarfin soja don samun iko a kan tsibirin.
Sanarwar da suka fitar ta ce dokar za ta tabbatar da cewa Greenland ba za a iya sayarwa ko ƙwace shi ba, kuma cewa duk wata mu’amala da ƙasar Denmark, wadda Greenland ke ƙarƙashin ikon ta dole ne ta bi dokokin ƙasa da ƙasa da kuma amincewar Majalisar Amurka.
Masu gabatar da kudirin sun ce hakan na da matuƙar muhimmanci domin kiyaye mutuncin dokokin kasa da kasa da kuma ‘yancin Greenland, tare da guje wa duk wani yunƙuri na amfani da ƙarfin soja ko siyasa wajen mallakar ƙasar.
Kudirin na zuwa ne a daidai lokacin da batun Greenland ya sake ɗaukar hankalin duniya, musamman bayan wasu maganganun Trump da ke nuna sha’awarsa kan muhimman albarkatu da matsayi na tsaro da Greenland ke da shi a yankin Arctic.
‘Yan majalisar sun yi ƙarin bayani cewa wannan doka ba wai tana adawa da hulɗar diflomasiyya kawai ba ce, har ma tana ƙarfafa cewa duk wata shawara game da Greenland dole ta kasance ta hanyar haɗin gwiwa da girmamawa ga ikon ƙasar da dokoki masu inganci.
A halin yanzu, ana sa ran wannan kudiri zai shiga cikin muhawarar majalisar kafin a yi yanke shawara kan ko za a amince da shi, yayin da batun ya janyo ce-ce-kuce tsakanin ‘yan siyasa da ƙungiyoyi masu sha’awar kare dokokin ƙasa da ƙasa.