Iran Ta Zargi Hukumomin Leken Asiri Na Waje Da Tada Rikici a Zanga-Zangar Da Ke Faruwa a Kasar

 Gwamnatin Iran ta zargi hukumomin leƙen asiri na ƙasashen waje, musamman Amurka da Isra’ila, da hannu wajen tada rikici da zanga-zangar da ke faruwa a ƙasar, tana mai cewa wasu daga cikin waɗanda ke jarogantar zanga-zangar sun samu horo ne daga wajen ƙasar da kuma taimako daga “mayaƙan waje.” 

Gwamnatin Iran

A jawabin da jami’an gwamnati suka yi a kafafen watsa labarai na gwamnatin, an ce an horar da wasu mutane a ciki da wajen Iran, tare da kawo wasu da ake kiran “’yan ta’adda” daga ƙasashen waje da suka kai hari kan wasu kasuwanni da wuraren ibada. Wannan ikirari na nuni da zargin cewa ƙungiyoyi da ke aiki a ƙarƙashin jagorancin hukumomin leƙen asiri na waje na ƙoƙarin gurgunta ikon gwamnatin Iran. 

Ministan harkokin wajen Iran ya mace cewa ƙasar na da hujoji na takardu dake nuna cewa Amurka da Isra’ila suna da hannu a cikin ayyukan “ta’addanci” da rikici da suka biyo bayan zanga-zangar, inda ya ce wasu jami’an leƙen asiri suna nan a fili a yayin bore. 

Gwamnatin ta kuma ce tana kallon rikicin a matsayin wani yunkurin kawo canjin gwamnati daga waje, ba wai ƙorafin cikin gida kawai ba. Wannan ya sa aka ƙara tsaurara matakan tsaro da kama masu zanga-zanga da ake zargi da aiki tare da “makiyan ƙasa.”

A gefe guda, masu sukar gwamnati da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam na ganin cewa zargin hukumomin waje wani dalilin kare kai ne daga ƙorafin jama’a kan matsin tattalin arziki da rashin adalci, kuma ba a gabatar da hujjoji masu kwararan gaskiya ba. Amma gwamnati na amfani da wannan zargi wajen ƙarfafa rigimar tsaro da dakile zanga-zangar. �

Post a Comment

Previous Post Next Post