SHIRIN KAWO KARSHEN YAKIN GAZA YA KAWO KARSHE

Wakilin Trump na musamman a Gaza ya sanar da ƙaddamar da mataki na biyu na shirin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

GazaA wannan matakin, za a kafa gwamnatin ƙwararru a Gaza, sannan za a ƙwance ɗamarar ƙungiyar Hamas, kuma sojojin Israila za su janye.

Zuwa yanzu dai Hamas ta ƙi amincewa ta miƙa makamanta, haka-zalika Isra'ila ta ƙi amincewa da ficewa baki ɗaya daga Gaza.

Yarjejeniyar da aka cimma na tsawon watanni uku na da rauni.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce Falasɗinawa fiye da 400 suka mutu a hare-haren Isra'ila tun bayan tsagaita wuta.

Post a Comment

Previous Post Next Post