Kotu A Pakistan Ta Yankewa Yan Jarida Hukuncin Daurin Rai-Da-Rai Kan Zanga-Zangar Goyon Bayan Imran Khan Ta 2023

 Wata kotu a Pakistan ta yankewa wasu ’yan jarida hukuncin ɗaurin rai-da-rai, bisa rawar da ta ce sun taka a zanga-zangar goyon bayan tsohon firaminista Imran Khan da ta ɓarke a shekarar 2023.

Pakistan

Hukumomin shari’a sun ce an same su da laifin tayar da tarzoma, ingiza jama’a zuwa tashin hankali da kuma karya dokokin tsaron ƙasa, bayan zanga-zangar da ta biyo bayan kama Imran Khan ta rikiɗe zuwa rikici a sassa daban-daban na ƙasar.

Gwamnati ta bayyana cewa zanga-zangar ta haddasa lalata kadarorin gwamnati da na soji, lamarin da ta ce ya zama barazana ga zaman lafiyar ƙasa. Kotun ta yi hukunci ne bisa dokokin yaki da ta’addanci na Pakistan.

Sai dai kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da na ’yan jarida sun soki hukuncin, suna cewa yana nuna takura wa ’yancin faɗin albarkacin baki da aikin jarida a ƙasar. Sun kuma yi kira da a sake duba shari’ar.

Lauyoyin waɗanda aka yankewa hukunci sun ce za su daukaka ƙara, yayin da batun ke ci gaba da janyo muhawara kan dimokuraɗiyya da ’yancin ɗan Adam a Pakistan.

Post a Comment

Previous Post Next Post