A ranar 1 ga watan Janairun 2026 ne ake sa ran sabuwar dokar haraji ta Najeriya za ta fara aiki wadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka wa hannu domin amincewa ta zama doka.
An dai ta tunanin cewa za a dakatar da fara aiwatar da harajin kafin sabuwar shekara sakamakon zarge-zargen cushe da aka yi wa dokar ta haraji, wadda aka ce ta bambanta da asalin wadda majalisar dokoki ƙasar ta amince da ita.A ranar 30 ga watan Disambar 2025 ne shugaba Tinubu ya sanar da cewa babu buƙatar dakatar da fara aiwatar da harajin domin hakan zai katse wa Najeriya burinta na samar da cigaban da ake buƙata.
Sai dai ya ce yana sane da irin zarge-zargen da ake yi dangane da cushe a dokar kuma yana aiki da majalisar dokokin ƙasar wajen samar da mafita.