Shugaban ƙasar Cuba, Miguel Díaz-Canel, ya yi kakkausar suka kan tsohon shugaban Amurka Donald Trump, bisa abin da ya kira ƙoƙarin murƙushe tattalin arzikin Cuba ta hanyar tsaurara takunkumai da matakan matsin lamba na siyasa da tattalin arziki.
Díaz-Canel ya bayyana cewa manufofin Trump, musamman waɗanda suka shafi takunkuman kasuwanci, kuɗi da zirga-zirga, an tsara su ne da gangan domin hana Cuba numfashi ta fuskar tattalin arziki, tare da jefa al’ummar ƙasar cikin ƙarin wahala. Ya ce waɗannan matakai ba wai suna cutar da gwamnati ba ne kawai, har ma suna shafar talakawa kai tsaye.
Shugaban na Cuba ya ƙara da cewa Amurka na amfani da ƙarfin ikon ta wajen hana Cuba hulɗa da kasuwannin duniya, da kuma tsoratar da kamfanoni da ƙasashe masu son yin mu’amala da Havana. A cewarsa, wannan salon siyasa na nuna rashin adalci da tauye ‘yancin ƙasashe masu cin gashin kansu.
Díaz-Canel ya jaddada cewa duk da wannan matsin lamba, Cuba ba za ta ja da baya ba, kuma al’ummar ƙasar sun saba da jurewa ƙalubale tun shekaru da dama na takunkumai. Ya ce gwamnati za ta ci gaba da neman hanyoyin da za su kare walwalar jama’a tare da ƙarfafa tattalin arziki ta hanyoyi na cikin gida da haɗin gwiwa da ƙasashen da ke goyon baya.
Wannan furuci na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da samun tsamin dangantaka tsakanin Cuba da Amurka, inda batun takunkumai da siyasar yankin Latin Amurka ke ci gaba da tayar da muhawara a matakin duniya.