Tattalin Arzikin Venezuela Ya Shiga Cikin Rashin Tabbas Bayan Daukar Maduro

 Tattalin arziƙin Venezuela ya shiga wani babban yanayi na rashin tabbas bayan da dakarun Amurka sun kama shugaban ƙasar Nicolás Maduro, abin da ya kawo mummunan tasiri kan tsarin kuɗi da siyasar ƙasar.

Venezuela

Rahotanni daga masana tattalin arziƙi sun nuna cewa ƙasar ta riga ta kasance tana fama da mummunan koma baya tun shekaru da dama, musamman a fannin man fetur  ginshiƙin tattalin arziƙinta, wanda yanzu ya faɗi ƙasa sosai sakamakon rashin zuba jari, cin hanci da kuma takunkumin Amurka. Har yanzu ba a san cikakken yadda tsarin tattalin arziƙin ƙasar zai tashi ba tun bayan ɗaukar Maduro.

Bayan ɗaukar shugaban, kasuwar kuɗi da hannayen jari ta nuna rudani, inda kadarorin tattalin arziƙin Venezuela ke wuyar hango makoma saboda rashin tabbas kan ikon gwamnati kan man fetur da sauran albarkatu. Wasu masu saka jari sun nuna cewa akwai dama ta farfaɗo da masana’antar man fetur idan aka samu kwanciyar hankali, amma har yanzu hauhawar farashi da rashin tabbas na ci gaba da damun tattalin arzikin. 

A cikin yanayin rikicin, al’ummar Venezuela na ɗaukar wannan lokacin da wani mataki na tashin hankali da ƙalubale, inda gurbataccen tsarin tattalin arziƙi, hyperinflation da ƙarancin ma’aikata suka ƙara rura wutar damuwa da fargaba a cikin al’umma.

A halin yanzu, gwamnati da hukumomi na ƙasar na ƙoƙarin tsayar da rikicin siyasa da tabbatar da ci gaban tattalin arziƙi, yayin da dama ke ganin cewa dawo da zaman lafiya da tsarin dimokuraɗiyya ne kawai zai iya kawo mafita mai ɗorewa ga Venezuela.

Post a Comment

Previous Post Next Post