Amurka Ta Ce Russia Ta Ba Iran Bayanai Don Kai Hari Kan Kadarorin Amurka

 Gwamnatin United States ta cewa Russia ta bai wa Iran bayanan sirri da za su iya taimaka mata wajen kai hari kan kadarorin sojan Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya. Jami’an Amurka sun ce suna sane da irin waɗannan rahotanni, amma sun jaddada cewa hakan ba ya shafar ayyukan sojojin Amurka a yankin.

Russia

Wasu majiyoyin leken asiri sun bayyana cewa ana zargin Russia ta ba Iran bayanai kan inda jiragen ruwan yaƙin Amurka, jiragen sama da sauran kayan soji suke a yankin. Sai dai jami’ai sun ce babu wata hujja da ke nuna cewa Moscow ta umurci Iran yadda za ta yi amfani da waɗannan bayanai.

Fadar White House ta amince cewa ta ji rahotannin, amma ta rage muhimmancinsu. Kakakin fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce zargin musayar bayanan sirri “ba ya kawo wani sauyi” domin hare-haren da Amurka ke kai wa Iran na ci gaba kamar yadda aka tsara.

Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya kuma bayyana cewa hukumomin leken asirin Amurka na sa ido sosai kan duk wata mu’amala tsakanin ƙasashen da ke da hannu a rikicin. Ya ce Amurka na sane da duk wani cigaba kuma tana la’akari da shi wajen tsara matakan sojinta.

Wannan lamari na zuwa ne a lokacin da rikici ke ƙara tsananta tsakanin United States, Israel da Iran, inda ake ci gaba da kai hare-hare da makamai masu linzami da jiragen yaƙi a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post