A watan Disambar da ya gabata, an kai wani yaro ɗan shekara huɗu mai suna Nitin Balasekar daga gundumar Sivaganga asibiti bayan ba shi zuma domin maganin ciwon ciki.
Bayan shan zumar, sai yaron ya suma, lamarin da ya sa aka garzaya da shi zuwa asibitin gwamnati na Sivaganga, inda ake ci gaba da kula da lafiyarsa.Shugaban Kwalejin Kiwon Lafiya ta Gwamnati da ke Sivaganga, Srinivasan, ya shaida wa manema labarai cewa abin da ya jawo matsalar shi ne sinadarin da ake kira botulinum wadda ake iya samu a cikin zuma.
A cewarsa, "wannan sinadarin na iya shafar ƙwaƙwalwa da jijiyoyin jiki, ta kuma kawo matsala ga numfashi da zagayawar jini."
Ya ƙara da cewa an saka yaron a kan na'urar taimaka wa numfashi tare da ba shi maganin riga-kafi na musamman da ake kira immunoglobulin.
Wannan lamarin ne ya dasa ayar tambaya ko za a iya bai wa yara musamman jarirai zuma?
Bincike daban-daban ya nuna cewa bai wa jarirai zuma nan da nan bayan haihuwa ko kafin a fara ba su nono al'ada ce da ta yaɗu a wasu ƙasashen Kudancin Asiya, ciki har da Indiya.
Haka kuma, binciken da aka wallafa a shafin intanet ta Babban ɗakin karatun kiwon Lafiya na Amurka ya nuna cewa bai wa yara ƙanana zuma ya zama ruwan dare a wasu ƙasashen yankin Gulf kamar Saudi Arabia.