Harın Drone Ya Tarwatsa Zirga-Zirgar Jiragen Sama A Dubai Yayin Da Iran Ke Ci Gaba Da Hare-Hare A Yankin Gulf

 Zirga-zirgar jiragen sama a Dubai International Airport da ke Dubai, a cikin United Arab Emirates, ta samu tangarda bayan wani harin jirgin mara matuƙi (drone) ya haddasa gobara a kusa da filin jirgin.

Dubai International Airport

Rahotanni sun ce dronen ya bugi wani tankin ajiye mai da ke kusa da filin jirgin, lamarin da ya jawo babbar gobara kafin jami’an kashe gobara su samu nasarar shawo kanta. Hukumomi sun ce ba a samu rahoton asarar rayuka ba, amma an dakatar da wasu jirage na ɗan lokaci saboda matsalar tsaro.

Bayan harin, an karkatar da wasu jirage zuwa Al Maktoum International Airport, yayin da kamfanin jiragen sama na Emirates da wasu kamfanoni suka jinkirta ko kuma suka soke wasu tafiye-tafiye.

Ana danganta harin da ci gaba da hare-haren drone da makamai masu linzami da Iran ke kaiwa a yankin Gulf, a yayin da rikici tsakanin Iran, United States, da kuma Israel ke ƙara tsananta, lamarin da ke shafar filayen jiragen sama, tashoshin mai da kuma hanyoyin kasuwanci a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post