Jami’an Tsaro a Bolivia Sun Kama Fitaccen Shugaban Harkar Miyagun Kwayoyi Sebastian Marset

 Jami’an tsaro a Bolivia sun kama fitaccen shugaban harkar miyagun ƙwayoyi Sebastian Marset bayan wani samame da ’yan sanda suka kai.

Sebastian Marset

Hukumomi sun ce an kama Marset ne a wani aiki na musamman da jami’an tsaro suka gudanar bayan dogon bincike da kuma farautar sa a ƙasashe daban-daban.

An dade ana neman Sebastian Marset, wanda ake zargi da jagorantar wata babbar ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi da ke aiki a sassan Kudancin Amurka.

Jami’an tsaro a Bolivia sun ce kama shi wani babban nasara ne a yaƙin da ƙasar ke yi da masu safarar miyagun ƙwayoyi, kuma bincike kan abokan hulɗarsa na ci gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post