Kasashen G7 za su Fara Bude Runbunan Ajiyar Man Fetur

Kasashe da dama na kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki G7 sun sanar da cewa za su buɗe wasu daga cikin manyan runbunan ajiyar man fetur da suke da su, a wani yunkuri na kwantar da hankula a kasuwannin makamashi na duniya, yayin da ake ci gaba da yaki da Iran.

Kasashen Japan, Austiriya da Jamus sun ce za su fitar da mai daga rumbunan ajiyar kasashensu.

Akwai kuma rahotannin da ke cewa hukumar kula da makamashi ta duniya IEA tana neman mambobinta talatin da biyu da su saki gangar mai aƙalla miliyan dari hudu. Idan hakan ya tabbata, zai zama babban shiga tsakani da hukumar IEA ta yi a kasuwar mai ta duniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post