Shugaban ayyukan jin-ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kira da a tsagaita wuta a Sudan ta Kudu, inda ya yi gargaɗin cewa karya dokokin ƙasa da ƙasa ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula aƙalla ɗari da sittin a cikin ƴan makonnin da suka gabata.
Volker Türk ya ce hankalinsa ya tashi na ganin ƙaruwar abin da ya bayyana da kisan-gilla da raba mutane da muhallansu.Wannan kiran na zuwa ne bayan dakarun gwamnati ta gwabza da masu goyon bayan dakataccen mataimakin shugaban ƙasar Riek Machar a garin Akobo da ke arewa maso gabashin ƙasar, birnin da sojojin ƙasar ke ƙara kutsawa domin mayar da shi ƙarƙashin ikon gwamnati.