An Fara Jawaban Karshe a Shari’ar da Elon Musk Ya Shigar Kan OpenAI

An fara sauraron jawaban ƙarshe a babbar shari’ar da attajirin fasaha Elon Musk ya shigar kan kamfanin OpenAI, wata shari’a da ake kallon ta a matsayin mai matuƙar muhimmanci ga makomar masana’antar ƙirƙirarriyar basira (AI).

kamfanin OpenAI

Musk, wanda yana daga cikin waɗanda suka kafa OpenAI a shekarar 2015, ya zargi kamfanin da kauce wa manufarsa ta asali ta samar da fasahar AI domin amfanin jama’a baki ɗaya ba tare da fifita riba ba. Ya ce OpenAI ta koma mai mayar da hankali ga kasuwanci da riba bayan haɗin gwiwarta da kamfanin Microsoft.

Lauyoyin Musk sun bayyana a kotu cewa OpenAI ta karya yarjejeniyar farko da aka kafa kamfanin a kai, inda suka yi zargin cewa an fifita anfani na kasuwanci maimakon buɗaɗɗiyar bincike da ci gaban AI cikin gaskiya.

A ɓangarenta, OpenAI ta musanta zarge-zargen, tana cewa tsarin kamfanin ya canza ne domin samun isassun kuɗaɗen da za su taimaka wajen haɓaka fasahar AI cikin aminci da tsaro. Kamfanin ya kuma bayyana cewa Musk ya san sauye-sauyen tsarin tun kafin ya fice daga kamfanin.

Ana kallon wannan shari’a a matsayin wadda za ta iya yin tasiri sosai kan yadda ake tafiyar da manyan kamfanonin AI, musamman game da batun buɗaɗɗiyar fasaha, riba, da kuma ikon sarrafa manyan fasahohin zamani.

Ana sa ran kotun za ta yanke hukunci bayan kammala jawaban ƙarshe daga lauyoyin ɓangarorin biyu.

Post a Comment

Previous Post Next Post