Jami’an Lafiya Sun Nuna Fargaba Kan Bullar Sabuwar Cutar Ebola a DR Congo

 Jami’an lafiya a nahiyar Afirka sun nuna matuƙar damuwa bayan sake ɓullar cutar Ebola a yankin Ituri da ke arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DR Congo), inda aka ruwaito daruruwan waɗanda ake zargin sun kamu da cutar da kuma mutuwar mutane da dama. 

DR Congo

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC) ta bayyana cewa an samu mutane 246 da ake zargin sun kamu da Ebola, yayin da mutum 65 suka mutu a yankin da cutar ta bulla. Gwaje-gwajen farko sun tabbatar da kwayar Ebola a cikin 13 daga cikin samfurori 20 da aka bincika. 

Masana lafiya sun ce akwai babban haɗarin yaɗuwar cutar zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Uganda da Sudan ta Kudu saboda yawan zirga-zirgar jama’a, matsalar tsaro, da kuma rikice-rikicen ‘yan bindiga da ke addabar yankin. 

Rahotanni sun nuna cewa wannan sabon ɓullar cutar na zuwa ne bayan kusan watanni biyar da aka ayyana kawo ƙarshen annobar Ebola ta baya a ƙasar. Haka kuma, masana sun bayyana cewa sabon nau’in cutar da aka gano na iya bambanta da nau’in Zaire Ebola wanda aka saba amfani da alluran rigakafi da magunguna a kansa, lamarin da ke ƙara tayar da hankali. 

Africa CDC da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na aiki tare da hukumomin Congo da ƙasashe maƙwabta domin ƙarfafa bincike, sa ido kan iyakoki, da kuma ɗaukar matakan gaggawa domin dakile yaɗuwar cutar. 

Post a Comment

Previous Post Next Post