An Kama Wani Tsoho Mai Shekara 60 Kan Zargin Lalata da Ƙaramar Yarinya a Bauchi

Jami’an rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi sun kama wani mutum mai shekara 60 mai suna Musa Garba bisa zargin lalata da wata yarinya ’yar shekara tara a yankin Magama Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toro ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Habib, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce mahaifin yarinyar ne ya kai rahoton lamarin a Hedikwatar ’Yan Sanda ta Toro a ranar Juma’a.

A cewar Habib, mahaifin yarinyar mai shekara 47 ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yaudari ’yarsa tare da kai ta wani buyayyen wuri a ranar 7 ga Mayu, 2026, da misalin ƙarfe huɗu na yamma.

“An karɓi rahoton lamarin a sashen ’yan sanda na Toro a ranar 8 ga Mayu, 2026. Mahaifin yarinyar ya bayyana cewa an yaudari ’yarsa tare da kai ta wani buyayyen wuri a ranar 7 ga Mayu, 2026, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma ta hannun Musa Garba, wanda ke zaune a unguwa ɗaya da su,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ya ƙara da cewa jami’an bincike na sashen Toro sun yi gaggawar cafke wanda ake zargin bayan samun rahoton.

Kazalika, kakakin rundunar ya ce yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, sannan ya kuma bayyana cewa ya sha aikata irin wannan mummunan aiki da yarinyar a lokuta daban-daban da wurare mabambanta.

Post a Comment

Previous Post Next Post