Dangote Ya Yi Watsi da Bukatar NNPCL na Ƙara Hannun Jari a Matatar Mai

Attajirin ɗan kasuwa ɗan Najeriya, Aliko Dangote, ya bayyana cewa kamfaninsa ya yi watsi da bukatar da Nigerian National Petroleum Company Limited ta gabatar na ƙara hannun jarinta daga kaso 7.25 cikin ɗari a cikin Matatar Mai ta Dangote.

Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Babban Jami’in Asusun Arzikin Ƙasar Norway, Nicolai. 

Wannan na zuwa ne yayin da binciken jaridar The PUNCH ya nuna cewa yawan man fetur da matatar mai ta dala biliyan 20 da ke Lekki ta samar ya kai lita biliyan 3.18 a zangon farko na shekarar 2026, yayin da shigo da fetur daga ƙasashen waje ya ragu sosai zuwa lita miliyan 965.52 kacal.

Binciken ya kuma nuna cewa matsakaicin farashin fetur daga matatar Dangote tsakanin watan Janairu zuwa Maris na shekarar 2026 ya kai kusan naira 1,000 kan kowace lita. Wannan na nufin cewa matatar ta samar da fetur da darajarsa ta haura naira tiriliyan 3.2 a kasuwar cikin gida cikin watanni ukun farko na shekarar.

Haka kuma, rikicin da ke tsakanin United States da Iran, wanda ya haddasa tangarɗa a ɓangaren man fetur da sauran fannoni, ya ƙara wa matatar Dangote kuɗaɗen shiga, sakamakon ƙaruwa da aka samu wajen fitar da kayayyakin man fetur da aka tace zuwa ƙasashen waje.

Dangote ya bayyana a hirar cewa an ƙi amincewa da bukatar NNPCL ta ƙara hannun jari ne saboda kamfanin na shirin shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari domin bai wa sauran ’yan Najeriya damar mallakar kaso a matatar.

An ruwaito cewa a shekarar 2021, NNPCL ta sayi kaso 7.25 cikin ɗari na hannun jarin matatar kan dala biliyan 1, tare da damar sayen sauran kaso 12.75 cikin ɗari kafin watan Yunin 2024. Sai dai daga baya kamfanin mai na ƙasa ya janye daga wannan shiri.

Post a Comment

Previous Post Next Post