DALILAN DA YA SA YAWANCIN HADARI KE SHIGOWA NAJERIYA DAGA GABAS

 DALILAN DA YA SA YAWANCIN HADARI KE SHIGOWA NAJERIYA DAGA GABAS

[Chad, Cameroon, Central Africa da Sudan]

 mafi yawan lokaci, hadari da ruwan sama da muke samu a Arewacin Najeriya suna tasowa ne daga gabas.

Hadari

👏 Fatan zaku mana Like da sharing domin Saura su amfana

Wannan ba haka kawai bane — akwai manyan dalilai kamar haka 👇

🌪️ 1. Hanyar iska ta damina (Wind flow)

Iskar damina tana motsawa daga gabas zuwa yamma, tana tura gajimare kai tsaye zuwa Najeriya.

🌡️ 2. Tsananin zafin yankunan gabas

Yankunan Chad, Cameroon da Central Africa suna da zafi sosai, wanda ke taimakawa wajen samar da gajimare masu nauyi da ƙarfi.

🌩️ 3. Haɗuwar iska mai zafi da mai sanyi

Iska mai zafi daga ƙasa + mai sanyi daga sama = hadari mai ƙarfi (instability).

🌫️ 4. Taruwar hadari kafin shigowa Najeriya

Hadari yana samun lokaci ya girma sosai a waɗannan yankuna kafin ya iso.

🌍 5. Tasirin Sudan

Wasu lokuta hadari daga Sudan na haɗuwa da sauran na Chad da Cameroon — hakan yana ƙara ƙarfin su sosai.

📌 A takaice:

Gabas ita ce babbar hanya da hadari ke bi zuwa Arewacin Najeriya.

⚠️ Lura:

Ba duk hadari bane ke isa Najeriya — wasu suna rauni a hanya, wasu kuma sukan zama manyan hadurra.

🔥 Ka kasance a shirye!

Hadari daga gabas na iya isowa cikin sauri fiye da yadda ake zato.

Post a Comment

Previous Post Next Post