France Ta Haramta Wa Itamar Ben-Gvir Shiga Kasar Saboda Cin Zarafin Masu Rajin Kare Hakki

 Gwamnatin Faransa ta sanar da hana ministan tsaron cikin gida na Isra’ila, Itamar Ben-Gvir, shiga ƙasar saboda abin da ta bayyana a matsayin cin zarafi da wulakanta masu fafutukar kai agaji zuwa Gaza. 

Jean-Noel Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noel Barrot, ya bayyana cewa Faransa ba za ta amince da barazana ko cin mutunci ga ‘yan ƙasarta da sauran masu fafutukar zaman lafiya ba. Matakin ya biyo bayan wani bidiyo da Ben-Gvir ya wallafa wanda ke nuna yadda aka tsare wasu masu fafutuka da Isra’ila ta kama daga jiragen ruwa masu ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza. 

Rahotanni sun nuna cewa masu fafutukar, waɗanda suka fito daga ƙasashe daban-daban na Turai, sun zargi jami’an Isra’ila da cin zarafi, wulakanci, da muzgunawa bayan kama su a tekun Mediterranean. Wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun ce an tilasta musu durƙusawa tare da ɗaure hannayensu yayin tsare su. 

Faransa ta kuma bukaci Tarayyar Turai ta ɗauki irin wannan mataki kan Ben-Gvir, inda wasu ƙasashen Turai suka fara kira da a kakaba masa takunkumi saboda kalamansa da ayyukansa masu tsauri. 

Lamarin ya haifar da suka daga ƙasashe da dama har ma daga wasu jami’an gwamnatin Isra’ila, ciki har da Firayim Minista Benjamin Netanyahu, wanda ya ce yadda Ben-Gvir ya tafiyar da lamarin bai dace da ƙimomin Isra’ila ba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post