Makinde Ya Ayyana Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a 2027 Ta Jam’iyyar APM

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasar Najeriya a zaɓen shekarar 2027 ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM).

Makinde

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin wani babban gangamin haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da APM da aka gudanar a dakin taro na Mapo Hall da ke Ibadan, babban birnin jihar.

Makinde ya ce lokaci ya yi da za a sake gina Najeriya, yana mai cewa:

“Lokacin sake farfaɗo da Najeriya ya yi. Saboda haka, a yau ni, Oluseyi Abiodun Makinde, na bayyana tsayawa takarar shugaban ƙasar Tarayyar Najeriya.”

Ya bayyana cewa halin da ƙasar ke ciki na ci gaba da taɓarɓarewa, lamarin da ya sanya mafi yawan ‘yan Najeriya cikin yanayin fafutukar rayuwa ta yau da kullum.

A cewarsa, jami’an gwamnati da ke da alhakin kula da walwalar jama’a sun yi watsi da nauyin da ke kansu.

Makinde ya ƙara da cewa:

“A cikin watannin baya-bayan nan, tambaya ɗaya ce ke yawan zuwa raina: ina za mu dosa daga nan? Shin haka ya kamata mu ci gaba a matsayin ƙasa?

“An matsa mana har bango da tunanin cewa za mu juya wa junanmu baya ko kuma mu gaji da rayuwa har mu kasa yin fito-na-fito.”

Gwamnan ya kuma yi watsi da zargin cewa jam’iyyun adawa ba za su iya haɗuwa ba, yana mai cewa:

“Sun ce jam’iyyun adawa ba za su haɗu ba, amma ina nan yau domin bayyana cewa wannan kuskuren hasashe ne. Adawa a Najeriya ba jam’iyya kawai ba ce, adawa ita ce talakan ɗan Najeriya da ƙasar nan ba ta yi masa aiki.”

Makinde ya ce haɗakar PDP da APM za ta bai wa ɓangaren PDP damar tsayar da ‘yan takara a dukkan matakai na zaɓen 2027.

“Saboda haka yau a Ibadan, an kafa haɗakar farko mai girma tsakanin PDP da APM.

“Wannan haɗin guiwar zai ba mu damar tsayar da ‘yan takara daga sama har ƙasa. Daga takarar shugaban ƙasa zuwa majalisun jihohi da duk sauran matakai.”

Tun da farko, Makinde ya jagoranci ɓangaren PDP na Taminu Turaki a Jihar Oyo wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da APM a matsayin wani shiri na haɗin gwiwa gabanin zaɓukan 2027.

Shi da shugaban jam’iyyar APM na ƙasa, Yusuf Dantalle, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin jam’iyyunsu.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, ana sa ran ‘yan takarar ɓangaren PDP masu neman kujerun gwamna, sanatoci, ‘yan majalisar wakilai da na majalisun jihohi za su fafata ne a ƙarƙashin inuwar APM maimakon PDP a zaɓen shekarar 2027.

Post a Comment

Previous Post Next Post