Tinubu Ya Gargadi 'Yan Jam'iyyar APC Game Da Zaben Fidda Gwani

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi kira ga ƴan jam'iyyar APC da su fita su kaɗa ƙuri'a a zaɓen fitar da ƴantakarar da za su wakilci jam'iyyar a babban zaɓen ƙasar, inda ya buƙace su da su gudanar da zaɓen cikin lumana.

Asiwaju Bola Ahmad Tinubu

A gobe Juma'a ne za a fara gudanar da zaɓen fitar da ƴantakarar APC, inda za a fara da zaɓen fitar da ƴatakarar majalisar wakilai.

"Mun assasa APC ne domin ci gaban al'umma da haɓaka dimokuraɗiyya da sadaukarwa. Wannan sadaukarwar ta taimaka mana wajen zama tsintsiya, don haka akwai buƙatar mu cigaba da ɗabbaƙa ta," in ji shi.

Ya ce zaɓe na cikin manyan ginshiƙan dimokuraɗiyya, sannan ya yi kira da a gudanar da zaɓen fitar da ƴantakarar a matsayin ƴanuwa.

"Dukkan ƴantakara da masu zaɓe dole su tabbatar da zaman lafiya, sannan su fifita muradun jam'iyyar da ma ƙasar baki ɗaya. Dole a kowace takara akwai wanda zai yi nasara, da wanda zai yi rashin nasara. Ina fata dukkansu za su dunƙule su yi aiki tare."

Tinubu ya kuma yi kira ga waɗanda za su yi nasara da su yi haƙuri su raka waɗanda suka yi nasarar, domin a cewarsa, " wanda ya yi nasara shi ne wanda ya yi haƙuri ya jira wani lokaci, ba wanda zai fasa kowa ya rasa ba."

Shugaban ya kuma ce waɗanda suka yi nasara ya kamata su ja kowa a jiki, "mu guji siyasa a mutu ko a yi rai wadda aka wuce lokacinta."

Post a Comment

Previous Post Next Post