Mene ne Hindutva, Kuma Mene ne Asalin Wannan Yunkurin Siyasar?

 Hindutva wata akida ce ta siyasa da al’adu da ke nuna cewa ƙasar India ya kamata ta kasance bisa al’adun Hindu, tarihin Hindu, da kuma kimar addinin Hindu. Kalmar “Hindutva” na nufin “Hindanci” ko “asalin Hindu,” kuma ɗan siyasa kuma marubucin India mai suna Vinayak Damodar Savarkar ne ya fi shahara wajen gabatar da ita a shekarar 1923 ta cikin littafinsa mai suna Hindutva: Who Is a Hindu? A cikin littafin, Savarkar ya bayyana cewa India ƙasa ce ta Hindu, kuma ya kamata a gina asalin ƙasar bisa tarihin da al’adun Hindu.

Hindutva

Asalin wannan aƙida ya samo tushe ne tun lokacin mulkin mallakar Birtaniya a India a ƙarshen ƙarni na 19 da farkon ƙarni na 20. A wancan lokaci wasu masu ra’ayin kishin ƙasa na Hindu sun fara ganin cewa akwai buƙatar haɗa kan mabiya Hindu domin kare al’adunsu da addininsu daga tasirin Turawan mulkin mallaka da kuma ƙaruwar tasirin siyasar wasu addinai kamar Musulunci. Wannan ne ya sa aka fara ƙungiyoyi da dama da suka rungumi ra’ayin Hindutva domin ƙarfafa kishin ƙasa bisa tsarin Hindu.

Daga cikin manyan ƙungiyoyin da suka yaɗa akidar Hindutva akwai Rashtriya Swayamsevak Sangh (RSS), wadda aka kafa a shekarar 1925 domin haɗa kan matasan Hindu da koyar da kishin ƙasa. Haka kuma jam’iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) ta zama babbar jam’iyyar siyasa da ke ɗaukar akidar Hindutva a matsayin ginshiƙinta. A yau, wannan jam’iyya ce ke mulkin India ƙarƙashin jagorancin Firayim Minista Narendra Modi.

Masu goyon bayan Hindutva suna ganin cewa wannan akida tana taimakawa wajen dawo da martabar al’adun Hindu da ƙarfafa haɗin kan ƙasar India. Sai dai masu suka suna zargin cewa Hindutva na iya haifar da wariya ga ƙananan addinai kamar Musulmai da Kiristoci, tare da barazana ga tsarin secularism wato raba addini da gwamnati wanda kundin tsarin mulkin India ya tanada. Saboda haka, Hindutva na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan batutuwan muhawara a siyasar India da ma duniya baki ɗaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post