Amurka Ta Kara Matsin Lamba Kan Cuba Bayan Ta Kakaba Wa Shugaba Diaz-Canel Takunkumi

 Gwamnatin United States ta ƙara matsin lamba kan ƙasar Cuba bayan ta sanar da ƙaƙaba takunkumi kan shugaban ƙasar, Miguel Díaz-Canel.

Cuba

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne saboda zargin take haƙƙin ɗan adam, murƙushe ‘yan adawa, da takaita ‘yancin faɗar albarkacin baki a Cuba.

Takunkumin ya haɗa da hana Diaz-Canel da wasu manyan jami’an gwamnati shiga Amurka tare da ƙuntata wasu harkokin kuɗi da alaƙa da gwamnatin Cuba.

Washington ta ce gwamnatin Cuba na ci gaba da kama masu zanga-zanga da masu sukar gwamnati tun bayan zanga-zangar da ta barke a ƙasar a shekarun baya saboda matsalolin tattalin arziki da ƙarancin abinci da wutar lantarki.

Sai dai gwamnatin Cuba ta yi Allah wadai da matakin, tana mai cewa Amurka na amfani da takunkumi wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gida na ƙasar.

Havana ta kuma zargi Washington da ƙara jefa tattalin arzikin Cuba cikin matsin lamba ta hanyar tsaurara takunkuman tattalin arziki da suka daɗe suna shafar rayuwar jama’a.

Masana siyasa sun ce wannan mataki na nuna yadda dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ke ci gaba da tsami duk da ƙoƙarin da aka yi a baya wajen kyautata alaƙa.

Rahotanni sun nuna cewa takunkuman na iya ƙara dagula matsalar tattalin arziki da Cuba ke fuskanta, musamman yayin da ƙasar ke fama da hauhawar farashi, ƙarancin kayayyaki, da matsalar makamashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post