Kotu Ta Yanke Wa Masu Garkuwa Da Mutane Hukuncin Kisa

Kotun Koli Ta tabbatar da hukuncin kisa ga wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane. Kotun Koli ta Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yanke wa wani da aka samu da laifin garkuwa da mutane a Jihar Delta, Chelynor Halim.

Kotu A Nijeriya

Alkalai biyar na Kotun Kolin sun yi watsi da  daukaka karar da wanda aka yankewa hukuncin ya shigar, tare da tabbatar da hukuncin da babbar kotun Asaba ta yanke masa tun a shekarar 2017.

Kotun ta samu hujjojin da suka nuna cewa Halim da wasu abokan aikinsa sun yi garkuwa da wata mata mai suna Joan Osemene a shekarar 2014, inda suka kwace mata katin ATM da kudi, sannan suka cire Naira 55,000 daga asusunta.

Bayan ta tsere daga hannun masu garkuwar, matar ta gane daya daga cikin wadanda suka sace ta lokacin da ta sake haduwa da shi, lamarin da ya sa aka kama shi tare da mika shi ga jami'an tsaro.

A hukuncin da Mai Shari'a Chioma Nwosu-Iheme ta karanta, Kotun Koli ta ce hujjojin da aka gabatar sun tabbatar da cewa Halim yana cikin wadanda suka aikata laifin, saboda haka ta tabbatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yanke masa.

Post a Comment

Previous Post Next Post