An yi musayar wuta mai ƙarfi a tsakiyar birnin Mogadishu gabanin wata zanga-zangar adawa da mulkin shugaban ƙasar Somalia, Hassan Sheikh Mohamud.
Tsohon Firaministan Somalia, Hassan Ali Khaire, ya zargi dakarun gwamnati da kai hari kan gidansa yayin da yake shirye-shiryen gudanar da zanga-zangar lumana tare da ‘yan adawa.
Rahotanni sun ce an ji karar bindigogi masu nauyi da kuma fashewar rokokin RPG a yankin Howl Wadaag, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin firgici. Wasu shaidu sun ce an kashe aƙalla mutum uku tare da jikkata wasu da dama.
Rikicin siyasar Somalia ya ƙara tsananta bayan shugaban ƙasa Hassan Sheikh Mohamud ya sanar da tsawaita wa’adin mulkinsa da shekara guda bayan wa’adinsa ya ƙare a watan Mayu. ‘Yan adawa da shugabannin yankuna sun yi watsi da matakin, suna zargin shugaban da ƙoƙarin ƙara karɓe iko.
Tsohon shugaban ƙasa, Sharif Sheikh Ahmed, shi ma ya soki harin, yana mai cewa ba zai hana jama’a gudanar da zanga-zangar da suke shirin yi ba.
Masu sa ido sun nuna damuwa cewa rikicin siyasar na iya ƙara haddasa rashin tsaro a Somalia, ƙasar da tuni ke fama da hare-haren ƙungiyar al-Shabaab da rikice-rikicen cikin gida.