Ɗan wasan tsakiya na ƙasar Denmark Cristian Eriksen na ci gaba da samun sauƙi.
Rahotanni sun nuna cewa, an sallame shi daga asibiti a biya, ya koma gida cikin iyalansa domin ci gaba da kula da lafiyarsa.
Sai dai majinyacin ya ce magoya bayansa su kwantar da hankalinsa yana cikin ƙoshin lafiya, ciwonsa a wannan karan ba irin na shekarar 2021 ba ne, wannan ya fi sauƙi sosai. Ya kuma miƙa godiya ga ɗaukacin al'ummar da suka taimake shi tun bayan da ya faɗi ana tsaka da buga wasan, ya yi godiya ga likitocin cikin fili, 'yan wasa da alƙalin wasa, da kuma likitansa da sauran al'umma da suka taya shi alhinin abin da ya faru.
A cikin wata takarda da Cristiano Ronaldo ya wallafa a shafinsa na Facebook ya jajanta wa Eric tare da ba shi shawarar ya haƙura da buga ƙwallo ya kula da lafiyarta, domin Lafiya Uwar jiki ce, sai da ita ake yin komai. Haka shi ma Thiery Henry tsohon ɗan ƙungiyar Arsenal ya ba Eric makamanciyar irin wannan shawarar.
Ku wace shawara za ku ba wannan ɗan wasa da ya faɗi a cikin fili ana tsaka da wasan ƙwallo karo na biyu a mabambanta lokuta saboda bugun zuciya?