Masu amfani da dandalin hasashen sakamakon abubuwa na duniya na Polymarket sun fara sanya kuɗaɗe domin hasashen wanda zai lashe zaɓen shugaban ƙasar Najeriya na shekarar 2027 kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Binciken da aka gudanar a dandalin ya nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ke kan gaba a hasashen masu caca, inda yake da kaso 68 cikin 100 na yiwuwar nasara, tare da cinikin da ya haura dala 14,823.
A matsayi na biyu akwai Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, wanda ke da kaso 25 cikin 100 na hasashen nasara da kuma cinikin dala 5,937.
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, yana matsayi na uku da kaso 1.5 cikin 100, bayan ya sha kaye wajen neman tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Haka kuma, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda aka bayyana a matsayin mataimakin Obi a takarar NDC, yana da ƙasa da kaso 1 cikin 100 na hasashen nasara, yayin da Omoyele Sowore ma ke da ƙasa da kaso 1 cikin 100.
Rahoton ya nuna cewa tun bayan fara wannan hasashe a ranar 2 ga Yuni, an gudanar da cinikayya da ta kai dala 28,677 cikin mako guda. Ana sa ran za a rufe hasashen ne a ranar 16 ga Janairu, 2027, ranar da aka ce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.
Dandalin Polymarket na amfani da tsarin saye da sayar da hannun jari na hasashe, inda masu amfani ke zaɓar “Yes” idan suna ganin wani ɗan takara zai yi nasara ko “No” idan suna ganin ba zai yi nasara ba.
Haka kuma, ƙimar hannun jarin hasashen tana canzawa bisa sabbin labarai, sauye-sauyen siyasa da kuma buƙata a kasuwa. Dandalin yana gudanar da mu’amalolinsa ne ta amfani da kuɗaɗen Internet na USDC a kan tsarin Polygon blockchain.
Baya ga siyasa da zaɓe, masu amfani da Polymarket na kuma sanya kuɗaɗe kan hasashen sakamakon wasanni, lambobin tattalin arziki, kyaututtuka na duniya da kuma kasuwar kuɗaɗen Internet.
