Jami'an Tsaro Sun Hallaka Shugaban 'Yan Ta'adda Kachalla Ibrahim Battijo a Kogi

Jami’an tsaron Najeriya sun yi nasarar kawar da wani da ake zargi da zama babban kwamandan 'yan ta'adda, Kachalla Ibrahim Battijo, yayin wani samame na hadin gwiwa da aka kaddamar a Jihar Kogi.

Haka zalika, harin ya tarwatsa muhimman rassan dakarun dake karkashin ikon Battijo, lamarin da ya gurgunta ayyukan kungiyar baki daya a yankin. Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa wannan gagarumar nasara na cikin rukunin ayyukan da ake ci gaba da yi na yaki da ta'addanci, fashi da makami, da sauran manyan laifuka masu alaka da zubar da jini, da nufin inganta tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Ana sa ran samun kararin bayanai daki-daki game da wannan samame daga bakin hukumomin da abin ya shafa nan ba da dadewa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post