Yadda Jagororin NADECO Suka Roki Janar Abdulsalami Ya Tsawaita Mulkin Soja A 1999

ABUJA, NIGERIA — Tsohon Shugaban Kasa na Mulkin Soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ya bayyana wani boyayyen al'amari dangane da komawar Najeriya tafarkin dimokuradiyya. Ya bayyana cewa wasu manyan jagororin fafutukar kwato dimokuradiyya, ciki har da mambobin kungiyar National Democratic Coalition (NADECO), sun taba rofansa a asirce da ya tsawaita wa'adin mulkin soja bayan sun gamsu cewa da gaske yake yi na mika mulki ga farar hula a shekarar 1999.

Wannan babban juyi a cikin tarihin siyasar kasar ya nuna cewa, ita kanta kungiyar NADECO da ta riga ta dade tana adawa da mulkin soja a lokacin marigayi Janar Sani Abacha, ta nemi a kara mata lokaci ne bayan ta fahimci cewa ba ta gama shirin tunkarar zabe da komawa tsarin mulkin farar hula ba.

Tsohon shugaban ya bayyana hakan ne a cikin littafin tarihin rayuwarsa (autobiography) wanda aka kaddamar a ranar Asabar, yayin bukukuwan murnar cikarsa shekaru 84 da haihuwa, wadanda aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Shaku Da Kuma Neman Alfarmar Da Aka Yi A Asirce

A cewar Janar Abdulsalami, da farko jagororin NADECO sun nuna shakku kan shirin mika mulkin da ya zo da shi, domin sun saba ganin yadda gwamnatocin soja na baya suka sha saba alkawari. To sai dai, zaran da suka gaza samun hujjojin nuna kuskure a tare da shi, kuma suka gamsu cewa gwamnatinsa za ta sauka a kan lokaci, sai wasu daga cikansu suka tunkare shi da batun tsawaita wa'adin.

"Bayan watanni biyu zuwa uku da kafa gwamnatina, sai wasu mambobin NADECO suka fahimci cewa ina da gaske game da ranar mika mulki," in ji Janar Abdulsalami.

"Sun ji cewa jirgi ya riga ya tsallake musu, don haka suke bukatar karin lokaci domin su tsara kansu a siyasance. Sun zo mini a matsayin kungiya inda suka bukaci da a tsawaita shirin mika mulkin."

Sai dai Janar Abdulsalami ya bayyana cewa ya yi fatali da wannan bukatar tasu, yana mai jaddada musu cewa ya riga ya dauki alkawari a gaban 'yan Najeriya da ma kasashen duniya na maida kasar tafarkin dimokuradiyya a cikin kayyadadden lokaci.

Jarabawar Gaskiya Da Matsin Lamba Daga Kasashen Waje

Domin gwada gaskiyar bukatarsu, tsohon shugaban ya kalubalanci jagororin na NADECO da su fito fili su bayyana wa duniya abin da suke nema.

"Na fada musu cewa idan za su rubuto mini wasika, kuma su sanar wa duniya a bayyane cewa sun nemi a tsawaita wa'adi, zan amince da hakan. Amma ba su taba aikata hakan ba. Kuma na riga na sani sarai ba za su iya ba," in ji shi.

Bugu da kari, tsohon Shugaban Kasar ya bayyana cewa matsin lambar na tsawaita mulkin sojan bai tsaya ga 'yan cikin gida ba kadai; har da wasu shugabannin kasashen waje wadanda suka yi amanna cewa gwamnatinsa ta dawo da tabbataccen zaman lafiya bayan mutuwar Abacha, da kuma sassauta takaddamar siyasa gami da takunkuman da aka kakaba wa kasar.

Duk da haka, ya jaddada cewa bai taba amincewa da ra'ayin tsawaita zaman sa a kan karagar mulki ba, domin Najeriya ta riga ta kai wani mataki da mika mulki ga farar hula ya zama dole kuma babu makawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post