Shirin Amurka Na Gina Cibiyar Killace Masu Alaka Da Cutar Ebola a Kasar Kenya Ya Haifar Da Zanga-Zanga

Shirin Amurka na gina cibiyar killace masu alaƙa da cutar Ebola a ƙasar Kenya ya haifar da zanga-zanga da fushin jama’a saboda mutane da dama na ganin shirin zai jefa rayuwarsu cikin haɗari.

Ebola

Ana shirin gina cibiyar mai gadaje 50 a sansanin sojin sama na Laikipia da ke garin Nanyuki domin karɓar ‘yan Amurka da aka yi zargin sun yi hulɗa da masu cutar Ebola a Democratic Republic of the Congo da Uganda.

Mutane da yawa a Kenya na fargabar cewa kawo mutanen da ka iya ɗauke da cutar Ebola zuwa ƙasarsu zai iya haddasa yaɗuwar cutar, duk da cewa babu wata cutar Ebola da aka tabbatar a Kenya a yanzu. 

Wasu masu zanga-zanga sun ce ba su fahimci dalilin da ya sa Amurka ba za ta kula da ‘yan ƙasarta a cikin ƙasarta ba, sai ta kawo su Kenya. Wasu ma sun bayyana hakan a matsayin nuna wariya ko raina ƙasashen Afrika. 

Ƙungiyoyin likitoci da masu fafutukar kare haƙƙin jama’a sun kuma soki yarjejeniyar saboda rashin bayyana cikakkun bayanai ga jama’a da kuma rashin tattaunawa kafin amincewa da shirin. 

Kotun Kenya ta dakatar da aikin cibiyar na ɗan lokaci tare da umartar gwamnati ta bayyana duk wata yarjejeniya da aka yi da Amurka kan shirin. 

Zanga-zangar da aka gudanar a Nanyuki ta rikide zuwa tashin hankali, inda rahotanni suka ce an kashe mutum biyu yayin artabu tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro. 

Shugaban Kenya, William Ruto, ya kare shirin yana cewa yana daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa tsarin kariyar lafiya da shirin tunkarar annoba. Amma masu adawa sun ce Kenya bai kamata ta zama wajen killace mutanen da wasu ƙasashe ba sa son karɓa ba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post