Kim Jong Un Ya Yi Kira Da a Fadada Makaman Nukiliya Cikin Sauri

 Shugaban ƙasar North Korea, Kim Jong Un, ya yi kira da a ƙara faɗaɗa makamashin nukiliyar ƙasar cikin abin da ya kira “exponential expansion” wato haɓaka makaman cikin sauri.

Kim Jong Un

Rahotanni sun ce Kim Jong Un ya bayyana hakan ne yayin wani taron da ya shafi manufofin tsaro, inda ya jaddada cewa ƙasar na buƙatar ƙara ƙarfin nukiliya domin kare kanta daga abin da ya kira barazanar ƙasashen waje.

Ya kuma umarci sojojin ƙasar da masana kimiyya da su hanzarta haɓaka fasahar makaman nukiliya da kuma inganta tsarin harba su, tare da ƙara yawan makaman da ake da su.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun tashin hankali a yankin Koriya, inda ƙasar ta South Korea da kawayenta ke ci gaba da gudanar da atisayen soji tare da Amurka.

Masu sa ido kan harkokin siyasa sun ce wannan furuci na iya ƙara tsananta takun saka tsakanin Pyongyang da Washington, da kuma ƙara damuwa a yankin Asiya.

Ƙasar North Korea ta dade tana fuskantar takunkumin ƙasashen duniya saboda shirinta na nukiliya, amma duk da haka tana ci gaba da gwaje-gwajen makamai da sabbin fasahohi.

Ƙasashen Yamma sun sha yin kira da a dakatar da shirye-shiryen nukiliyar, suna mai cewa hakan na barazana ga zaman lafiya a duniya, yayin da Pyongyang ke cewa makaman nata na kare kai ne kawai.

Post a Comment

Previous Post Next Post