Kotun Koli Ta Umarci Isra’ila Ta Bai Wa ICRC Damar Ziyartar Falasdinawan Da Ke Gidajen Yari

 Kotun ƙoli ta Israel ta yanke hukunci cewa dole ne gwamnati ta bai wa ƙungiyar agaji ta Red Cross ta duniya (ICRC) damar ziyartar Falasɗinawan da ake tsare da su a gidajen yari.

ICRC

Hukuncin ya zo ne bayan ƙorafe-ƙorafe daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da iyalan fursunoni, waɗanda suka ce an hana ICRC damar ganin wasu fursunonin Falasɗinawa tun bayan fara rikicin Gaza.

Kotun ta bayyana cewa hana ƙungiyar damar ziyartar fursunoni na iya karya dokokin ƙasa da ƙasa da kuma haƙƙin ɗan adam, musamman ma dokokin Geneva da suka shafi kula da fursunoni yayin rikici.

Ƙungiyar International Committee of the Red Cross (ICRC) na taka muhimmiyar rawa wajen duba yanayin rayuwar fursunoni, tabbatar da samun kulawar lafiya, da kuma sauƙaƙa hulɗa tsakanin fursunoni da iyalansu.

Masu kare haƙƙin ɗan adam sun dade suna zargin Isra’ila da tsare dubban Falasɗinawa a cikin mawuyacin hali, ciki har da tsare mutane ba tare da shari’a ba a ƙarƙashin abin da ake kira “administrative detention”.

Gwamnatin Isra’ila ta ce wasu takunkuman tsaro ne suka sa aka takaita ziyarar a wasu lokuta, tana mai cewa ana ɗaukar matakan kariya ne saboda yanayin yaƙi da rikicin tsaro.

Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun yi maraba da hukuncin kotun, suna cewa zai taimaka wajen ƙara sa ido kan yadda ake mu’amala da fursunoni da kuma kare haƙƙinsu.

Rahotanni sun nuna cewa dubban Falasɗinawa na ci gaba da zama a gidajen yarin Isra’ila, yayin da batun fursunoni ke ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan batutuwan rikicin Isra’ila da Falasɗinu.

Post a Comment

Previous Post Next Post