Matatar Man Aliko Dangote Na Shirin Zama Mafi Girma a Duniya

 Katafariyar matatar man Aliko Dangote na ci gaba da faɗaɗa ayyukanta, yayin da kamfanin ya sanar da ƙara ƙarfin tace ɗanyen mai daga ganga 650,000 zuwa ganga 700,000 a kowacce rana. 

Matatar man Aliko Dangote

Rahotanni sun nuna cewa matatar, wadda ke jihar Lagos a ƙasar Nigeria, ta riga ta kai cikakken ƙarfin aikin da aka tsara mata tun farko, kuma yanzu ana ƙoƙarin ƙara yawan man da take tacewa domin ta zama ɗaya daga cikin manyan matatun mai a duniya.

Kamfanin Dangote Industries ya bayyana cewa wannan ƙarin aiki na cikin wani babban shiri na faɗaɗa matatar zuwa ganga miliyan 1.4 a rana cikin shekaru masu zuwa. 

Masana harkokin makamashi sun ce wannan ci gaba zai ƙara ƙarfin Nigeria wajen rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje, tare da ƙarfafa fitar da kayayyakin mai zuwa sauran ƙasashen Afrika da duniya baki ɗaya. 

Tun bayan fara aiki, matatar Dangote ta zama muhimmiyar cibiyar samar da fetur, dizal da man jiragen sama, musamman a lokacin da ake fama da matsalolin samar da makamashi a wasu sassan duniya. 

Post a Comment

Previous Post Next Post