1. Yadda za ka auna bugun zuciyarka a gida
Juya tafin hannunka sama Wanda kake so ka auna.
Sanya yatsunka biyu na daya hannun naka a gefen wuyan hannun dakake aunawa daga sama.
Kaduba hotan da muka saka a kasa sabida ka fahimci abunda muke nufi!!
Ka dan matsa yatsun naka biyun a hankali har sai ka ji wani abu yana bugawa kamar “duk-duk-duk.”
Da zarar ka ji bugun, sai ka duba agogonka ko stopwatch dinka na wayar ka ka saita shi na minti daya.
Ka kirga duk bugun da ka ji na tsawon dakika 60 watoh minti daya.
Idan yana kasa da 50 ko sama da 100, ko kuma bugun yana dan tsallakewa (kamar ya tsaya sannan ya ci gaba) ko bada tazara yana da kyau ka ga likita.
